Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Raguwar Barazanar Harin Da Birtaniya Ke Fuskanta.


Police officers carry equipment while investigating a crime scene where one man was killed in Woolwich, southeast London May 22, 2013.

An kama mutun na biyu da ake zargin kai hari a Birtaniya, wannan ne yasa mahukuntar kasar suka cean sassauta barazanare kai harin da kasar ke fuskanta

Burtaniya ta sassauta matakin barazanar karin ta'addancin da ake fuskanta a kasar daga "mai rikitarwa " zuwa "mai tsanani," bayan da 'yan sanda su ka kama mutum na biyu da ake zargi a harin ta'addancin da aka kai a wata tashar karkashin kasa ta jirgin kasa a London.

Sakatareniyar Harkokin Cikin Gida Amber Rudd ta ce kamu na biyu wata alama ce cewa an samu abin da ta kira, "kyakkyawan cigaba" a binciken da ake yi kan harin ta'addancin nan na ranar Jumma'a wanda ya raunata mutane 30, wadanda zuwa yanzu duk an sallame su daga asibiti imbanda mutum guda.

Mataki "mai tsananin" na nufin hukumomin Burtniya sun yi imanin cewa akwai yiwuwar kai wani harin sosai, a yayin da kuma "mai rikitarwa" ke nufin kusan lokaci ne kawai ake jira hari na gaba ya auku.

'Yan sanda sun ce sun damke wani mutum dan shekaru 21 da haihuwa a unguwar Houslow da ke Yammacin London, inda anan ne filin jirgin saman Heathrow na London ya ke, ana sha biyun daren asabar sauran 'yan dakikoki.

Tun da farko a ranar ta Asabar, an damke wani matashi dan shekaru 18 da haihuwa a Dover mai tashar jirgin ruwa, inda ake tafiya daga Burtaniya zuwa Faransa.

Facebook Forum

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG