Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Raguwar Cin Zarafin Al’umma Da ‘Yan Kato Da Gora Ke Yi a Najeriya


'Yan Kato Da Gora da aka yaye a jihar Filato

Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce an sami raguwar cin zarafin al’umma da ‘yan kato da gora keyi, yayin gudanar da aikinsu na tsaron al’umma.

Shugaban sashen gudanarwa da ayyukan tsaro na MDD a Najeriya, Mathew Alao, ya bayyana hakan yayin yaye wasu ‘yan kato da gora da aka fi sani da civilian JTF su 123 daga jihar Borno, a cibiyar koyar da dabarun shugabanci da zama ‘dan kasa na gari, dake Shere Hills a jihar Pilato.

Jami’in MDD ya ce a baya, ‘yan kato da goran na aiwatar da hukunci ne ba tare da la’akari da doka ba, amma tun da suka fara samun wannan horo, sukan mika wa hukumomi duk wanda suka kama don gudanar da bincike da aiwatar da hukunci.

‘Yan kato da goran sun sami horo ne kan sasanta al’umma da inganta zamanta kewa da sana’oi da kuma dabarun dakile tashe-tashen hankali a Arewa maso Gabas.

Domin Karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:02 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG