Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shawarci Najeriya Ta Maida Karfi kan Yin Anfani da Hasken Rana


 Babatunde Fashola ministan ayyuka da makamashin Najeriya
Babatunde Fashola ministan ayyuka da makamashin Najeriya

Yayinda wasu ke ganin ya kamata Najeriya ta koma yin anfani da gawayi wasu masana na ganin maida karfinta kan anfani da hasken rana shi ne zai samar ma kasar isasshiyar wutar lantarki domin cigaba

Wani masanin masana'antu Mr. Emmanuel Nwankwo yace dole ne Najeriya ta koma yin anfani da gawaji ko kwal wajen farfado da masana'antunta kamar yadda aka yi can baya.

A cewarsa dakatar da yin anfani da kwal ya biyo bayan gano man fetur ne a Najeriya lamarin da kuma ya mayar da hannun agogo baya wajen durkusar da masana'antu.

Amma yayinda Mr. Nwankwo ke son a koma yin anfani da kwal wajen samar da wutar lantarki a Najeriya wasu kuwa na ganin yin anfani da hasken rana shi ne ya fi wa kasar a'ala saboda kwal ba zai taimaka wajen farfado da masana'antu ko tattalin arzikin Najeriya ba..

Injiniya Awal Ibrahim na cibiyar kananan masana'antu a Najeriya yana mai cewa inda gwamnati ta kashe kashi daya na biliyoyin Nera da ta kashe wajen samar da wutar lantarki kan hasken rana da tuni kasar ta warke.

Kafin kasar ta koma ga dogaro ga man fetur ta dogara ne akan kwal da ake hakowa a jihar Enugu.

Acewar Injiniya Awal dole ne a koma kan hasken rana da iska da dai sauransu kafin a samu masalaha da karancin wutar lantarki domin idan lantarki bai wadatu ba ba za'a iya yin wasu abubuwa da dama ba.

Anfani da hasken rana da iska wajen samar da wutar lantarki baicin tabbatar da samar da isasshiyar wutar zasu kuma kiyaye gurbata muhalli. Kwararowar hamada zai ragu saboda za'a daina ko rage sare bishiyoyi ana makamashi dasu.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG