Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shirya Yin Maci Don Yaki Da Cutar Dajin Mama A Abuja


Kungiyoyi masu zaman kansu na lamuran kiwon lafiya sun dage kan kamfen din yaki da cutar dajin mama ko sankarar mama.

Wasu shararrun taurarun fina finan Nollywood irin su Joke Sylva da Francis Duru da sauransu, sun shirya wani maci a tsakanin unguwar Wuse 2 zuwa Maitama a karshen makon nan don wayar da kawunan al’umma kan illar cutar da kanyi sanadiyar mutuwar mata da yawa, musamman ma a yankunan karkara.

Matar gwamnan jihar Kebbi, Dakta Zainab Bagudu, likatar yarace wacce kuma ke bunkasa kamfen din yaki da cutar ta sankarar mama, haka kuma itace ta shirya wannan gangami da za a yi.

A cewar Dakta Zainab, ba a gane ciwon da wuri har sai yayi tsanani, wannan kuma shine wata na Goma da ake gudanar da wannan shirin, mata da yawa sun fito da ciwon kuma yayi tsanani. Kasancewar tsanani da yawan ciwon yasa ake rasa rayukan mata da dama a Najeriya.

Dakta Zainab, tace ana rasa rayukan mata a Najeriya sama da sauran kasashen da suka ci gaba, idan aka duba cikin mata 100 da suka kamu da cutar a kasashen, 95 suna rayuwa, sabanin kasashen da basu ci gaba ba wanda cikin 100 guda biyar ne kawai zasu rayu.

A Najeriya akwai na’urorin gwajin wanan cuta har guda Bakwai, amma ko da yaushe guda Daya ne ke aiki. Akwai matsalolin dayawa game da ganewa da tantacewa ko mace na dauke da wannan cuta a da kuma maganinta. Yanzu kuwa akwai ita wannan na’ura jihohin da dama a Najeriya, kuma ana son da zarar mace ta kai shekaru 40 ta rika zuwa ana gwada ta.

A cewar wani magidanci Adamu Attahiru, wanda kuma ya shaida illar wannan cuta yace, akwai wata matar abokinsa da sankarar mama tayi sanadiyyar ajalinta, tun da ta kamata wasa wasa ana ta magani har zuwa wasu jihohi uku daga karshe aka yanke ‘daya, daga baya aka koma a yanke na biyu karshen rayuwarta kenan.

Wani bincike da aka gudanar a shekara ta 2012, mata 52 kan kamu da cutar sankarau ta mama daga cikin mata 100,000 yawancin matan a karshe suka sukan rasa ransu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

XS
SM
MD
LG