Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tabbatar Da Kisan Wasu Mutane Biyu a Filato


Daya daga cikin jiragen yaki masu saukar ungulu da aka tura Filato kwanan baya

Kaito, jahar Filato ta fara murmurewa daga tashin hankalin kwanan baya kenan sai kawai aka samu labarin kashe wasu masu sana'ar sayar da kayan miya su biyu. Wannan ya sake tuna ma al'ummar jahar Filato illar fitina, wacce idan ta tashi kwantar da ita sai an hada da matukar imani da tsoron Allah.

A wani cibaya, an kashe wasu mutane biyu a garin Barikin Ladi na jahar Filato, wadda a ‘yan shekarun nan ta shiga sahun jahohin da ke fama da tashe-tashen hankula. Kashe mutanen biyu ya biyo bayan dan kwanciyar hankalin da aka samu, bayan mummunar fitinar da ta tashi kwannan baya, wadda ta yi sanadin asarar rayuka da dama.

An kashe mutane biyun, wadanda masu sana’ar sayar da kayan miya ne, ranar Lahadi. Hasali ma, tuni kungiyar ‘yan kayan miya ta jahar Filato ta ce kashe wadannan mambobin na ta biyu da aka yi, wani koma baya ne ga jahar ta Filato, wadda har ta fara murmurewa kafin nan.

To sai dai duk da wannan abin takaici na kashe wadannan mutane biyu, har yanzu wasu shugabannin jama’a na kiran da akai zuciya nesa. Mataimakin shugaban kungiyar masu sayar da kayan gini a jahar ta Filato, Garba Ibrahim, ya yi kiran da a yi hakuri a yafe ma juna.

Ga dai Zainab Babaji da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG