Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An tabbatar da mutuwar mutune 11 a jihar Niger


Hatsarin kwale lwale

An tabbatar da mutuwar mutane goma sha daya a wani hadarin jirgin kwale kwale a jihar Niger

An tabbatar da mutuwar mutane 11 a wani hadarin jirgin ruwan kwale kwale a jihar Niger.

Bayanai sun tabbatar da cewa hadarin kwale kwalen ya faru ne a daren Litinin a kogin Bunu dake yankin karamar hukumar Sarkin Pawa.

Rahotanin sun baiyana cewa wadanda lamarin ya rutsa dasu illahirinsu mata ne. Rundunr yan sandan jihar Niger ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, ASP Bala El Kana yace har yanzu, basu samu cikakken bayanin abinda ya faru ba, amma suna gudanar da bincike,

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Niger, ta tura jami'anta domin kai dauki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:08 0:00

XS
SM
MD
LG