Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Takaita Zirga-zirga a Arewacin Amurka Da Malaysia


An dauki sabbin matakan takaita zirga-zirga a Arewacin nahiyar Amurka da Malaysia, a yayin da kuma dokar hana ketara kan iyakar kasashen Tarayyar Turai ta fara aiki.

Duk hakan na faruwa dai-dai lokacin da gwamnatoci ke neman hanyar shawo kan yaduwar shu'umar cutar murar nan ta coronavirus.

Yayin da Amurka ta sanar cewa za ta rufe kan iyakar Arewacin kasar da Canada na wucin gadi ga jigilar duk wani abun da bai zama dole ba, matafiya sun yi cinkus a kan iyakokin shiga Turai.

Kana yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a fadin duniya ya nufi dubu 200, kuma yawan wadanda cutar ta kashe ya wuce 7,500

Kasashen Turai ma, sun rufe iyakokinsu ga masu tafiyar da bata da muhimmanci, amma ga ma’aikata da direbobin manyan motoci dauke magani kofa a bude take.

Facebook Forum

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG