Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tarwatsa Taron Manema Labarai Na APC a Sakatariyar 'Yan Jarida a Kaduna


Taron Manema Labarai da wasu 'yan jam'iyyar APC suka shirya a sakatariyar 'yan jarida a Kaduna

Wasu matasa sun tarwatsa taron manema labarai da 'yan APC da basu gamsu da abun da suka kira dauki dora a zaben wakilai da aka yi ba, da suka kira a sakatariyar 'yan jarida dake Kaduna lamarin da ya kaiga lalata kaya tare da jima wani rauni.

Rikicin zabo wakilan da zasu wakilci reshen Kaduna a wajen yiwa jam'iyyar APC ta kasa kwaskwarima ya fantsama zuwa sakatariyar 'yan jarida ta jihar Kaduna.

Rigima ta barke ne daidai lokacin da zababbun 'yan majalisun jam'iyyar ta APC suka halarci sakatariyar 'yan jarida domin yin karin haske game da zaben da suka ce an yi dauki dora.

To saidai kafin mahalarta taron su kare wasu matasa suka kutsa wurin taron inda suka dinga dukan ababen hawa suna jefe-jefe har suka jima wani dan jarida Malam Lawal Muhammed rauni.

Mal. Lawal Muhammad, dan jarida da aka jima rauni
Mal. Lawal Muhammad, dan jarida da aka jima rauni

Amma duk da hayaniyar sai da mahalarta taron suka kammala taronsu.

Sanata Suleman Usman Hunkuyi yana mai cewa su da suka taru basu gamsu da yadda aka zabi wakilan da zasu yiwa kundun tsarin mulkin jam'iyyar gyaran fuska ba. Yace dukansu zabensu aka yi kuma su wanene basa son a yi zaben fidda wakilan zuwa gyaran kundun tsarin mulkin jam'iyyar?

Inji Sanata Hunkuyi idan zaben fidda wakilan da zasu gyara kundun tsarin mulkin jam'iyyar ya gagara to yaya za'a yi zaben kananan hukumomi? Yace dalili ke nan da hankalinsu ya tashi suka taru. Sun kira uwar jam'iyya ta duba lamarin ta kuma yiwa 'yan jama'ar jihar Kaduna adalci.

Shi ma Sanata Shehu Sani da ya kasance a taron yayi tur da yadda matasa suka kutsa taron domin tarwatsashi. Yace taronsu na nunawa mutanen Kaduna ne cewa ba zasu yadda da murdiya ba. Yace sun kori jam'iyyar PDP, sun zageta da rashin yin adalci amma yau gashi APC tana aiwatar da duk abubuwan da suka zargi PDP da yi.

To saidai wani bangaren na jam'iyyar ta APC yace an bi ka'idoji wajen zaben wakilan. Onarebul Tanko Salisu Solo wanda yayi magana a madadin jam'iyyar yace basu ji dadin kutsowar da matasa suka yi wurin taron ba.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG