Accessibility links

Shiga Abuja zai yi wuya a ranaku uku da za'a yi ana gudanar da taro akan tattalin arziki na duniya a babban birnin Tarayya.

Za’a fara taron na duniya akan tattalin arziki na duniya a Abuja har na tsawon kwanaki uku daga Laraba zuwa Juma'a.

Wannan yazo daidai da lokaci da Najeriya ke tunkahon cewa tafi kowace kasa arziki a nahiyar Afirka, kuma ta ashirin da shida a duniya, wannan ya numa kamar Najeriya tana kokarin nunawa duniya cewa ita ma ta fara tasowa kuma ta na da yanayi mai inganci na daukan nauyin shi wannan taro.

Sannan kuma da bada dama ga masu zuba hannayen jail su shigo kasar domin zuba wadannan hannayen jali.

Tuni ma jami’ai sun fara yarda farfagandan cewa duk rikice-rikicen da akeyi basu shafan tattalin arziki ko kuma zuba hannayen jali a Najeriya.

Jami’an ‘yan sanda dubu shida ne za’a yi amfani dasu domin tabatar da tsaro a yayi wannan taro na yini uku,wannan shine karo na farko da ake amfani da jami’an masu wannan yawan.

Kazalika ‘yan sanda sun fida sanarwa na kara tsaurara matakan tsaro domin shigowa cikin Abuja,wanda ya biyo bayan bada hutu a wadannan ranaku a babban birnin taraiya Abuja.

Don haka shiga Abuja zai yi matukar wuya indan ba taron mutu za halarta ba,
Shi kansa masaukin bakin inda za’a sauke masu halartar taron an sake masa fasali wadansu daga cikin ma’aikatan ma an basu hutu,kuma baza a shiga da mota wajen taron ba.
XS
SM
MD
LG