Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsaurara Matakan Tsaro A Filayen Jiragen Saman Arewacin Najeriya


Filin Jirgin Saman Kaduna
Filin Jirgin Saman Kaduna

Gwamnatin Najeriya ta ba da umarnin kara tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen sama da ke Arewacin kasar, biyo bayan wani farmaki da wasu ‘yan bindiga suka kai a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Kaduna, inda suka yi awon gaba da wasu ma’aikatan filin jirgin.

Shugaban hukumar jiragen saman kasar ta FAAN, Captain Rabiu Yadudu, ya ce tuni da aka cika umarnin na gwamnati, ta hanyar kara jami’an tsaro da matakan shiga, kazalika da tsaron ma’aikata a filin jirgin na Kaduna da sauran filayen jiragen Arewacin Najeriya.

A ranar Juma’a ne da dare, wasu ‘yan bindiga suka suka kai hari a gidajen ma’aikatan filin jirgin na Kaduna, inda rahotannin suka bayyana cewa sun yi awon gaba da mutane 9, da suka kumshi ma’aikatan filin jirgin da kuma wasu iyalansu.

Filin Jirgin Saman Kaduna
Filin Jirgin Saman Kaduna

Rahotannin sun bayyana cewa maharani sun sami shiga gidajen ma’aikatan ne ta hanyar babban titin gudun fanfalaki na filin jirgin, inda kuma suka kai har safiyar Assabar suna gudanar da farmakin na su.

Yadudu ya ce jami’ansa na aiki tare da jami’an tsaro da kuma gwamnatin jihar Kaduna domin ganin an sako mutanen da aka sace, inda ya ce tuni da ayarin suka soma tattara bayanan sirri na ganin an samo hanyar magance sake aukuwar irin wannan lamarin.

Captain Rabiu Yadudu, Shugaban hukumar FAAN
Captain Rabiu Yadudu, Shugaban hukumar FAAN

Ya kara da cewa rahoton bincike akan irin wannan harin da aka taba kaiwa a bara, ya kara taimaka musu wajen tsara matakan tunkarar irin wannan kalubalen.

Shi kuwa shugaban hukumar sararin samaniya ta Najeriya (NAMA), Captain Fola Akinkuotu, ya bayyana damuwa akan cewa fiye da sao’i 24 bayan sace mutanen, ‘yan bindigar ba su tuntubi hukumar ko wasu makusantan ma’aikatan ba.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG