Masu fashin bakin siyasa a jamhuriyar Nijer sun fara bayyana matsayinsu game da yadda suke kallon matakin tsige ministan kudin kasar Masa’udu Hasumi daga mukaminsa, a wani lokaci da ake jita-jitar fuskantar rarrabuwar kawuna a jam’iyyar PNDS mai mulki.
Wasu ‘yan kasar na alakanta matakin na shugaba Isuhu Mahamadu da wani furici da ministan ya yi kwanan nan da nufin kare kasar Faransa daga zargin ci gaba da yiwa kasashen Afirka mulkin mallaka.
Wani mai nazarin al'amuran yau da kullum Abdurahman Alkasum, ya ce Shugaban kasa na da hurumin yin haka bisa ga kundin tsarin mulki, abin da ya fi jan hankali a cewar Abdurahaman, shi ne duk da cewa ministan da shugaba Isuhu Muhammadu na da kusanci hakan bai hana shi tsige shi ba.
Ya kuma ce ba ya tunanin nuna sha’awar tsayawa takara ne ya janyo daukar wannan matakin kamar yadda wasu ke tunani.
Ga karin bayani cikin sauti.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 01, 2023
Kamaru Ta Cire Tallafin Man Fetur
Facebook Forum