Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Umurci Sufeta Janar Na 'Yan sandan Nigeria Ya Koma Jihar Benue Da Zama


IBRAHIM K. IDRIS, sabon babban sifeton 'yansandan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya baiwa sufeta janar na 'yan sandan Nigeria umurnin ya koma jihar Benue da zama har sai tsaro ya inganta a jihar

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya umurci sufeta janar na ‘yan sandan Nigeria da ya koma jihar Benue da zama har sai tsaro ya inganta.

Shugaban ya bada wannan umurnin ne jim kadan da kammala ganawar su da Gwamnan jihar ta Binuwe.

Da yake wa wakilin sashen Hausa Karin bayani,mai Magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu yace shugaban ya damu kwarai da gaske da abinda ke faruwa a jihar ta Benue.

Shima Gwamnan jihar Benue ya shaidawa manema labarai cewa yazo fadar shugaban kasa ne domin yayi wa Shugaba Buhari Karin bayani.

Ga Umar Faruk Musa da Karin bayani 4’09

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:23 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG