WASHINGTON, DC —
Jama’a assalamu alaikum, Yankin Wukari ya sha fama da tashe-tashen hankula masamman tsakanin alumar Jukun da Hausawa da ma Fulani a cikin makonin da suka gabata.
Sau tari, irin wannan rikici kan rikida ya sama fadar kabilanci ko kuma na addini wadda hakan ke sanadiyar salwantar rayuka da dukiyoyin alumar yakin wadanda basu san haw aba bale sauka.
Sai dai yanzu wasu sun wunkuro domin magance wannan matsalar, inda aka samu wasu Musulmai, suka amsa gayyatar, da wani mai bushara, yayi masu na zuwa cin abincin kiristimeti.
Fata dai shine Allah ya kawo fahimtar juna a tsakanin alumomin yakin na Wukari, domin kwanciyar hankali da ci gaban yankin.