Gidan Radiyon muryar Amurka, da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta kasar Amurka, sun gudanar da wani taron fadakarwa akan mahimmancin yin riga kafi ga yara da kuma mata masu juna biyu a garin Kontagora, dake jihar Neja.
Taron dai ya samu hakartar mata masu dinbin yawa da suka saurari jawabai daga kwararro akan kiwon lafiya, da suka hada da Dr, Muhammad Usman, wanda yake Darakta ne a ma’aikatar lafiya jihar Neja.
Yace “ Mun yi matukar farin cikin zuwa da wannan taro da aka yi, masamman gidan Radiyon muryar Amurka, da ta kawo mana wannan taro, don kasan abun idan aka ce ga yadda yake shine ma rika kafin da kuma fatan wadanda aka yi domin su zasu yi amfani dashi.”
Daga bisani dai an raba gidan sauro, da kayan yara da kuma riguna masamman ga matan da suka amsa tabbayoyi daga jami’an kiwon lafiya.