Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yankewa James Holmes hukuncin rai da rai


James Holmes (na biyu daga hagu) da ya kashe mutane a Silma

An yankewa mutumin nan James Holmes hukuncin daurin kare kukanka na rai da rai a gidan wakafi. Sakamakon budewa jama’a wuta da yayi a wani gidan Silmar Colorado dake wajen garin Denver anan Amurka.

Ya bude wuta akan mai uwa da wabi a lokacin da jama’ar suka sakankance suna kallon majigin wani film din Batman mai The Dark Night Rises, inda a take ya kashe mutane 12 da kuma raunata guda 70.

Holmes dan shekaru 27 da ya guji karatu, bai nuna wata nadama ba a lokacin da aka yanke masa hukuncin, hasali ma ya nuna halin ko in kula ne a lokacin da iyalan wadanda ya kashe suke bayyana takaicin raba su da iyalansu.

Lauyan mai laifin wato Holme dan shekaru 27 da ya yi watsi da karatu, ya yi ta kokarin nunawa kotu cewa mai laifin na fama da ciwon haukar rashin sanin dama balle hagu, amma kokarin nasa ya ci tura.

Inda masu gabatar da kara suka tabbatar da cewa James ya san abin da yake yi tunda har ya iya tsara yadda zai aikata wannan ta’asa ta hanyar tsarawa a rubuce a kundin ruce-rubucensa. Sannan yayi amfani da toshe kunnensa da abin jin sautin da ya kunna kida mai kara a lokacin da yake harbin jama’a.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG