Shugaba Barack Obama yayi rokon samun zaman lafiya tsakanin Isira'ila da Palasdinawa. Shugaban yayi wannan roko ne wajen wani gangamin tunawa da mutumin daya sadaukar da ransa domin a samu zaman lafiya, tsohon Prime Ministan Isira'ila Yitzhak Rabin.
Shugaba Obama ya yiwa dubban yan Isira'ila da suka yi bikin rayuwar Rabin jiya Asabar a birnin Tel Aviv ta faifan vidiyo kusan shekaru ashirin bayan wani BaYahude mai ra'ayin rikau wanda baya kaunan samun zaman lafiya tsakanin Isira'ila da Palasdinawa yayi masa kisan gilla.
Mr. Obama yace a wadannan kwanaki da suke zama masu wuya ga Palasdinawa da Isira'ila da kuma yankin ga baki dayansa, rayuwar Yitzhak da kuma abubuwan da yayi begen ganin sun faru, har yanzu suna tare da mu. Yace abinda ya fadawa wancan taro gaskiya ne. Yace zuwan su domin bikin rayuwar Yitzhak ya nuna cewa ko tantanma babu mutane suna begen ganin an samu zaman lafiya, basu kaunar tarzoma.
Tsohon shugaban Amirka Bill Clinton wanda yayi aiki kai tsaye tare da marigayi Yitzhak Rabin yaje birnin Tel Aviv shi da kansa kuma shima ya yi magana a jiya Asabar. Bill Clinton ya fadawa taron cewa mataki na gaba zai tantance ko sun yanke shawarar shin Yitzhak Rabin yayi daidai daya ce tilas su zaune tare da makwaptanta ku, kuma ku baiwa 'ya'yansu dama.
A wani wuri dabam a kasar ta Isira'ila, jiya Asabar Palasdinawan da suke yi zanga zanga sun fafata da sojojin Isira'ila a yayinda dubban mutane suka halarci jana'izar matasan Palasdinawa guda biyar a Hebron. Sojojin Isira'ila ne suka kashe su lokacinda suka daba ko kuma suke kokarin dabawa Yahudawa wuka.
Isira'ila ta rike gawarwarkin matasan, sai a ranar Juma'a ta bayar.
Shugaba Barack Obama yayi rokon samun zaman lafiya tsakanin Isira'ila da Palasdinawa. Shugaban yayi wannan roko ne wajen wani gangamin tunawa da mutumin daya sadaukar da ransa domin a samu zaman lafiya, tsohon Prime Ministan Isira'ila Yitzhak Rabin.