Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Garkuwa Da Mutane 15 A Jihar Taraba


Masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa sun addabi yankin Takum da kuma sauran kananan hukumomin jihar Taraba, inda su ka yi awon gaba da mutane da dama wadanda kawo yanzu ba a san inda su ke ba.

Yanzu haka jama’ar Jihar Taraba na barci da ido daya a bude, sakamakon matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a jihar, lamarin da ke hana jama’a kwana a gidajensu.

Kuma wannan matsalar tafi Kamari ne a yankin Takum da kuma wasu kananan hukumomin jihar.

Wani mazaunin yankin Takum ya tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutane goma sha biyar a yankin nasu, ciki har da wani mai gidan mai da aka yi garkuwa da shi sati biyar da suka shige, inda masu garkuwar suka nemi a basu Naira miliyan dari domin su sako shi.

Kamar yadda wani mazaunin yankin na Takum ya tabbatar, an ba wa masu garkuwa da mutane kudin amma daga bisani sun nemi a kara musu adadin kudin da suka karba tun da farko.

Shugaban kungiyar kare hakkin dan’adam na jihar Taraba, Kwamared Gambo Dawud, ya ce wannan garkuwa da mutane da ake yi domin neman kudin fansa yana damunsu, sannan ya yi kira da gwamnatin jihar Taraba da kuma gwamnatin tarayyar Najeriya da su dau mataki domin magance wannan matsala da ta addabi mutanen jihar.

Shima kwamishinan ‘yan sandan jihar Taraba, Alkassim Usman, ya kira taron manema labarai inda ya nuna wasu da aka kama da ake zargi masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu, a karkashin Ofireshan Cika Aiki da rundunar ta fara.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG