Wani gidan yin gwanjon kayayyakin tarihi a birnin Paris ya yi biris da kiran da hukumomin Najeriya suka yi masa na kada ya yi gwanjon wasu kayayyakin tarihin kasar.
Gidan gwanjon da ake kira Chritie's ne ya sayar da kayayyakin tarihin.
A baya wani malamin jami’a, Farfesa Chika Okeke- Agulu da ya sha alwashin ganin an mayar da kayayyakin zuwa kasarsu ta asali ya nemi da a dakatar da gwanjon.
Farfesan wanda ke koyarwa a sashen nazarin kayayyakin tarihin Afirka da na bakaken fata da suka zo Amurka a jami’ar Princeton, ya ce, “wadanda suke tunanin wannan batu ya bi ruwa, su kwan da sanin cewa batun bai kare ba.”
Farfesa Okeke-Agulu, wanda ya kirkiro wani maudu’i a shafin Twitter mai taken #BlackArtsMatter - wato kayayyakin tarihin bakaken fata na da muhimmanci, ya kara da cewa sai inda iya karfinsa ya kare a wannan fafutuka da ya sa a gaba.
Kalaman Farfesan na zuwa ne bayan gwanjon kayayyakin tarihin da gidan gwanjon ya yi a ranar 29 ga watan Yuni, wanda ya hada har da wasu kayayyakin tarihin Najeriya har da wasu na ‘yan kabilar Igbo guda biyu, wadanda aka sayar da su akan kudi dalar Amurka dubu 239,000
Wannan alwashi da malamin ya sha na ganin an mayar da kayayyaki, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta wasu kiraye-kirayen neman a mayar da wasu kayayyakin tarihin Afirka wadnada watakila kwato su aka yi zamanin mulkin mallaka ko kuma a lokacin yake-yake.
Sai dai cikin wata sanarwa da gidan gwanjon na Christie’s ya aikawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ce, ta hanyar halal ya mallaki kayayyakin tarihin ya kuma sayar da su bisa yadda doka ta tanada.
Facebook Forum