Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alex Ekwueme


Jana'izar Alex Ekwueme

Mashahuran 'yan Najeriya ciki harda mataimakin shugaban kasa Parfessa Yemi Osinbanjo ne suka yi jawabi a hidimar bizinar

A ranar jumma'a aka yi hidimar jana'izar tsohon mataimakin shugaban Najeriya Dr. Alex Ekueme,. Yay mataimakin shugaban kasa a zamanin jamhuryar ta biyu. Alex Ekueme, shine mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Shehu Shagari.

Da yake magana a haduwar, mataimakin shugaban Najeriya Parfessa Yemi Osinbajo, ya yaba da irin gudumawar da Dr. Ekueme ya bayar a ci gaban Najeriya ta ko wane fanni da ya taba.

Haka shima da yake magana, tsohon babban sakataren kungiyar kasshe renon Ingila, Dr. Emeka Anyaoku, yace marigayin ya taka rawar gani a fannonin rayuwa a uku muhimmai, a siyasar Najeriya, ta kasa-da-kasa- da kuma taimakon marasa galihu.

Da yake hira da wakilin Sashen Hausa AlphonsusOkoroigwe, tsohon ministan albarkatun ruwa na Najeriya, Barrister Mukhtari Shagari, ya bayyana mutuwar Alex Ekueme, a zaman babban rashi ba ga iyalansa ba kadai, amma kasa baki daya.

Ya yaba da dottaku da halin mutuntawa da suka yi aiki da mahaifinsa, tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari.

Gwamnoni na da dana yanzu, ministoci da dubun dubatan jama'a ne suka yi cicirindo a harabar cocin da aka yi hidimar, a garin Oko cikin karamar hukumar Orumba ta Arewa,inde aka binne shi.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG