Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi jana'izar mataimakin gwamnan jihar Borno


Taswirar Nigeria dake nuna jihar Borno cikin launin dorawa

Asabar da yamma aka yi jana'izar mataimakin gwanan jihar Borno Alhaji Zannah Umar Mustapha

An yi jana'izar mataimakin gwamnan jihar Borno, Alhaji Zannah Umar Mustapha a ranar Asabar da yamma, bayan da aka yi jigilar gawar sa daga Yola, jihar Adamawa.

Mataimakin gwamnan ya rasu Asabar a Yola, inda yaje ya wakilci gwamnan jihar Borno wajen bikin yaye dalibai da kuma ziyarta yan gudun hijira yan jihar Borno da suka arcewa rikicin Boko Haram

Wakilin sashen Hausa ya aiko da rahoto cewa mutane da yawan gaske, ciki harda manyan jami'an tsaro ne suka halarci jana'izar.

Mutanen da aka zanta dasu sun baiyana kyakywar halayar marigayin da suka baiyana shi akan wanda baya riko, tare da fatar Allah zai gafarta masa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG