Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi shirin kai hari New York


Magajin garin birnin New York Michael Bloomberg
Magajin Garin New York yace wadanda ake zargi da kai hari akan masu tseren fanfaleke a birnin Boston sun yi shirin kai hari birnin New York a wurin da ya fi cinkoson mutane da ake kira Time Square.

Magajin garin Michael Bloomberg ya fada ranar Alhamis cewa wanda yake raye yanzu Dzhokhar Tsarnaev ya fada ma masu bincike shi da wansa Tamerlan sun shirya su tuka mota zuwa New York su kara tada bama-bamai. Tamerlan ya mutu a dauki ba dadi da suka yi da yan sanda yayin da aka capke Dzhokhar kwana daya bayan mutuwar wansa.
Bloomberg yace birnin New York, musamman ma wurin da aka kai har aka kuma rushe dogayen gine-ginen nan biyu a shekara 2001 lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusa da dubu uku, wuri ne da yan ta’ada zasu so su sake kai hari.

A wata sabuwa kuma a can kasar Rasha iyayen mutanen biyu da ake zargi sun ce yayansu basu kai hari da ya kashe mutane uku kuma ya raunata 250 ba a birnin Boston.

Mahaifiyarsu ta zargi hukumomin Amurka da yi ma Tamerlan kashin gilla. A taro da manema labarai a garin Makhachkala iyayen, wato Anzor Tsarnaev da matarsa ta da Zubeidat sun ce kage aka yi wa yayansu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG