Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Taro Kan Bukatar Kare 'Yan Jarida Daga Tuhuma a Nijar


Jamal Khashoggi, wani babban dan jaridar da aka kashe a baya bayan nan.
Jamal Khashoggi, wani babban dan jaridar da aka kashe a baya bayan nan.

A shekarar 2010 ne gwamnatin jamhuriyar Nijer ta dauki matakin kare ‘yan jarida daga barazanar zuwa kurkuku saboda dalilai masu nasaba da aikin jarida, to sai dai shekaru 10 bayan sa hannu kan wannan takarda, har yanzu ana fuskantar turjiya ganin yadda ake ci gaba da garkame ‘yan jarida saboda bada labarin da bai yi wa mahukunta dadi ba. Dalilin kenan da cibiyar ‘yan jarida ta Maison de la Presse ta shirya taro domin nazari akan wannan al’amari, inji sakarenta mai kula da yada labarai Souleymane Brah.

Wannan na faruwa ne wata 1 kacal bayan da majalisar dokokin jamhuriyar Nijer ta bai wa gwamnatin kasar izinin sauraren hirarakin jama’a a waya ko yin kutse a kafafen sada zumunta.

Wata alkaliya dake fafitikar kare hakkin dan adam Malama Goge Gazibo Maimouna ce aka gayyato domin baje wa mahalarta wannan taro abubuwan da wadanan dokoki suka kumsa.

World Press Freedom Day.
World Press Freedom Day.

Alkaliya Goge ta ce, "Mu masana doka muka tsara wadanan dokoki wadanda mafi yawan lokuta ake dukanku da su ko a bugi ‘yan kasa da su. Dokar hukunta masu batanci a kafafen sada zumunta tana daya daga cikin dokoki mafiya tsanani a Nijer haka kuma tana daga cikin dokoki mafiya sarkakiya. Kwararru ne suka tsara ta to amma yana da kyau a matsayinku na ‘yan jarida ku iya bambanta wadanan dokoki biyu."

Halin ko in kula da mafi yawan ‘yan jarida ke nunawa dokokin da suka shafi aikin jarida a nan cikin gida, na daga cikin manyan dalilan da ke sanadin aika ‘yan jarida gidan yari a nan Nijer, inji editan jaridar la Roue de L’histoire, Ibrahim Moussa.

Ga wakilin Muryar Amurka Sule Barma da cikakken rahoton:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG