Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Wa Fadar Vatican Kutse


Fafaroma Francis a Fadar Vatican
Fafaroma Francis a Fadar Vatican

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa masu satar bayanai ‘yan kasar China sun yi ta yin kutse a jerin na’urar kwamfutocin Fadar Vatican tun daga watan Mayu.

Ana ganin cewa wannan wani yunkuri ne na yin leken asiri gabanin wata muhimmiyar tattaunawa da Cocin Roman Katolika za ta yi da kasar China mai bin tsarin kwaminisanci.

Cocin Vatican
Cocin Vatican

Jaridar ta ruwaito cewa wannan kutse da wani kamfanin tsaron yanar gizo mai zaman kansa na Amurka mai suna Recorded Future ya gano, ya kasance karon farko da aka kama masu satar bayanai dumu-dumu suna kutse akan Vatican da wani rukunin wakilan fadar da ke zaune a Hong Kong, wanda ke tattaunawa da kasar China kan matsayin Coci a kasar ta Sin.

Jaridar ta ce, kwararu a fannin tsaron yanar gizon na Recorded Future suna zaton masu satar bayanan suna yiwa gwamnatin Sin aiki ne.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG