Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa Kananan Yara Miliyan Daya Rigakafin Kyanda A Jihar Jigawa


Ana yiwa kananan yara rigakafin cutar kyanda

Gwamnatin jihar Jigawa tayi wa kananan yara sama da miliyan daya rigakafin cutar kyanda, a cikin ayyukan makon lafiya na 2013 da aka yi a jihar

Gwamnatin jihar Jigawa tayi wa kananan yara sama da miliyan daya rigakafin cutar kyanda, a cikin ayyukan makon lafiya na 2013 da aka yi a jihar.

Bisa ga bayanin dake dauke da rattaba hannun Alh. Mati Ali, an yiwa makon lakabi “mata masu shayarwa, da jarirai domin lafiyarsu.”

Ali yace, anyi wannan rigakafin a wurare dari biya da saba’in da shida a jihar. Ya kara da cewa, an shirya za’a yiwa yara fiye da miliyan daya rigakafin, an taimaki kananan yara dubu 956,169 da abincin gina jiki.

Bisa ga cewashi an kuma yiwa mata 92, 961 bayani kan shayar da mama da tsabtar wurin zamansu. Yace, “Fiye da ma’aikata 3,000 ne suka taimaka a wannan aikin. Aikin ya samu ne ta wurin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da ma’aikatar lafiya ta kasa (NPHDA).

Ya kara cewa, an dauki wannan matakin ne domin rage mutuwar kananan yara, kariyar cutar kyanda da sauran cututtuka dake kashe kananan yara, da kuma inganta aiki a wannan fannin.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG