Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matar Gwamnan Jihar Lagos Ta Nemi A Ceci Rayukan Kananan Yara


Yara suna wasa

Matar gwamnan jihar Lagos, Mrs. Abimbola Fashola, tayi kira ga sauran kungiyoyi dake sashen lafiya a kasa gaba daya, da su taimaka wajen rage mutuwar kananan yara

Matar gwamnan jihar Lagos, Mrs. Abimbola Fashola, tayi kira ga sauran kungiyoyi dake sashen lafiya a kasa gaba daya, da su taimaka wajen rage mutuwar kananan yara.

Uwargidan gwamnan tayi wannan kiran ne a wajen bukin kaddamar da wani dakin shan magani da wata kungiya mai zaman kanta da ake kira “Family Care Association” ta gina a lagos.

Mrs Fashola ta kara cewa, ana bukatar daukar dukan matakan da suka kamata a yunkurin shawo kan ko kuwa rage mutuwar yara da shekarunsu suka gazabiyar, da kuma mata masu ciki a Najeriya.

Mrs Abimbola Fashola, tayi kira ga mata masu ciki da masu shayarwa, suyi amfani da asibitocin da aka yi musu domin a rage mutuwar yara. Ta bayyana cewa, gwamnati ta samar da kayan aiki a asibitai da nufin ganin dukan al’ummar jihar Lagos sun sami kyakkyawar kulawa da kuma jinya a cikin dukan halin da suke ciki.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG