Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yiwa 'Yan Matan Chibok Liyafar Komawa Gidajen Iyayensu da Zuwa Karatu

'Yan matan Chibok da aka kubutar daga hannun 'yan ta'addan Boko Haram da suka yi garkuwa dasu tun ranar 14 ga watan Afirilun shekarar 2014 da suka sacesu daga makarantar sakandaren 'yan mata dake garin Chibok, sun samu wayarwa kuma gwamnatin tarayya ta dauki nauyin karatunsu.

Bayan sun samu horaswa da kwantar masu da hankaulansu biyo bayan irin ukubar da suka sha a hannun 'yan ta'ddan Boko Haram da suka sacesu a makarantarsu dake Chibok ranar 14 ga watan Afirilun shekarar 2014, yanzu zasu koma karatu da yin cudanya da iyayensu da sauran 'yanuwansu.

Gwamnatin tarayya wadda ta dauki nauyin karatunsu ta yi masu liyafar bankwana kafin su tafi makarantun da aka samar masu kamar yadda za'a gani a wadannan hotunan

Domin Kari

XS
SM
MD
LG