Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Gwamnatin Edo da Cin Zarafin Nakasassu


Nakasassu

Cibiyar Kare Hakin Bil Adama ta zargi gwamantin jihar Edo da cin zarafin nakasassu.

A wani taron manema labarai a birnin Kano daraktan cibiyar kare hakin bil Adama Barrister Audu Bulama Bukarti yace rahotanni dake zuwa hedkwatarsu na nuna halin kunci da nakasassu da gwamnatin ta tsare suke ciki.

Daraktan yace an karyawa mutanen 'yancinsu na bil Adama domin an kamasu an hanasu ganin 'yanuwansu da lauyoyinsu da abokansu. Bayan haka ba'a basu abinci ba an kuma ajiyesu a wurin da bai kamata a ajiye mutum ba.

Gwamnatin jihar Edo ta ki kaisu kotu cikin awa 24 kamar yadda doka ta tanada. Maganar cewa za'a mayardasu jihohinsu wata karya kundun tsarin mulkin kasa ne domin yaba duk dan Najeriya damar zama koina a cikin fadin kasar kuma babu wanda ya isa ya ci zarafinsa.

Cibiyar ta kare hakin bil Adama tace ya kamata gwamnatin jihar Edo ta sani cewa ba duka mutanen da ta kama ba ne mabarata. Banda haka akwai matakan da gwamnati zata shimfida kafin hana bara. A jihar babu dokar da ta hana bara. Idan ma akwai dokar sai an bi ka'idoji. Bata yiwuwa a je a kama mutum cikin gidansa. Ita gwamnatin Edo ta karya duk wasu ka'idoji. Kundun tsarin mulki bai ba wata ma'aikata ikon kama wani ba sai dai 'yansanda.

Cibiyar ta baiwa gwamnatin Edo kwanaki biyu ko su saki mutanen su kuma basu hakuri su kuma biyasu diya ko kungiyar ta ruga kotu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG