Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Magoya Bayan APC da Kona Kasuwa


Kasuwa
Kasuwa

Dagacin Gona, a karamar hukumar Akko, cikin jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Nasiru Sa’id, ya zargi magoya bayan dan takarar Gwamna, a inuwar jamiyyar APC, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya, da kona ofisoshin jamiyyar PDP, da shagunan kasuwa a garin na Gona, da kuma lalata masa motar sa ta shiga.

Jami’in hulda da jama’a, na dan takarar jamiyyar APC, a jihar Gombe, Alhaji Kabiru Muhammad, ya nisata magoya bayan dan takarar da aikata abin da ake zargin su akai.

Ya kara da cewa a lokacin da suka shiga garin na Gona sun tarar da wuta na ci a garin saboda haka ya ya za’a ce magoya banyan dan takarar APC, ne suka kona.

Siyasar Gombe -3'34"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

XS
SM
MD
LG