Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Mayakan Kurdawa da Sa Yara Aikin Soji a Syria


Wasu mayakan Kurdawa.

Kungiyar gwagwarmayar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch yau Laraba ta bayyana cewa mayakan Kurdawa a Syria na cigaba da amfani da yara a fagen yaki, duk da sunyi alkawarin kawo karshen haka shekara daya da ta wuce.

Human Rights Watch tace kungiyar mayakan YPG ta samu cigaba wajen dena amfani da yara a matsayin sojoji, amma kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa sun tattara shedun dake nuna cewa akwai yara 59 da suke ayyukan soji, ko aka saka suyi aikin soja a halin yanzu.

Kungiyar Human Rights tace ta tabbatar da gaskiyar wannan lamari har sau bakwai bayan tattaunawa kai tsaye da iyalan wasu yaran. Ta kara cewa kungiyar YPG to mayar da martani akan zarge-zargen inda tace tana fuskantar kalubale mai tsanani na kawo karshen amfani da yara a matsayin sojoji saboda fadan Syria, wanda a halin yanzu an share sama da shekaru 4 ana yi.

Mayakan Kurdawa na daga cikin kungiyoyi masu yawa dake fafatawa a yakin Syria, wanda a cikinsa akwai dakarun gwamnati, da kungiyoyin ‘yan tawaye kamar Free Syrian Army, da kuma mayakan sa kai kamar IS da Nusra masu alaqa da al-Qaida.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG