Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Sojojin Sudan Ta Kudu Da Kashe Wasu Mutane 60


Sojojin Sudan ta Kudu

Kungiyar rajin kare ‘yancin bil’adama ta Amnesty International ta zargi sojojin Sudan ta Kudu da laifin kashe wasu mutane guda 60 hade da yara ta hanyar makaresu a cikin irin katuwar Kwantenar da ake dakon kayayyaki da ita.

A rahoton da Kungiyar mai matsuguni a birnin Landan dake Birtaniya, tace ya kamata a zakulo wadanda suka yi wannan aika-aikar a kuma gurfanar da su gaban kuliya. Amnesty ta bayyana cewa abin ya faru ne a birnin Leer da ke kasar.

Inda sojojin gwamanati suka wadanan nan ‘yan kulle ‘yan talikan a cikin wannan katafaren bangajin daukar kayan ne, aka kuma ajiye a harabar wata cocin Katolika. Shedu da dama sun ce sun ga lokacin da sojojin ke ta kakaba mutanen a cikin kwantenar.

Shedun gani da idon sun kara da cewa, sun ji lokacin da wadannan bayin Allah ke ta kuka da kururuwar neman dauki daga cikin inda suke kulle da ba ko ‘yar tagar da numfashi zai shiga ya fita. Bayan sa’oi 24 duk mutanen sun mutu in ka dauke mutum 1 da ya sha da ransa, amma Gwamantin kasar ta musanta zargin.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG