Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zargi Wani Likitan Dabbobi Da Dasa Ruwan Hodar Iblis Cikin Karnukan


Likitan Dabbobi da karnuka
Likitan Dabbobi da karnuka

Andres Lopwz Elorza likitan dabbobi an zargeshi da fede cikin karnuka goma ya dasa musu ruwan hodar iblis tun a kasar Spain kana ya shigo dasu Amurka, idan laifin ya tabbata zai iya samun hukumcin daurin rai da rai ko akalla zaman gidan kaso na shekaru goma

Wani likitan dabbobi bai amsa laifin cewa ya fede wasu karnuka kuma ya dasa musu ruwan hodar iblis domin kawowa nan Amurka ba.

An gabatar da Andres Lopez Elorza a wata kotu dake birnin New York jiya talata bayan an taso keyar sa daga kasar Spaniya, yanzu haka dai an tsare shi ba tare da bada belin sa ba.

Muddin aka tabbatar da wannan laifin kansa to zai huskanci hukuncin zaman gidan yari har na tsawon shekaru 10 ko kuma daurin rai-da-rai.

Mai gabatar da kara yace Lopez Elorza ya dinke wani fakitin hodar iblis a cikin wasu nau’in karnuka wadanda aka sawo su cikin jirgin saman fasinja zuwa birnin New York. Sai dai a lokacinda ake kokarin fitar da pakitin daga jikin karnukan suka mutu.

Hukumar yaki da safaran miyagun kwayoyi ta Amurka tace karnuka 10 aka samu a wata gona a kasar Colombia lokacin da aka kai sumame gonar a shekarar 2005, ukku daga cikin karnukan da aka samu, sun mutu sakamakon alluran miyagun kwayoyin da akayi musu. Tun daga lokacin Lopez Elorza ya shiga wasan buya da jami’an tsaro.

A wuri daya kuma mahunkutar kasar Pakistan sun tuhumi wani jami’in tsaro dake aikin ofishin jakadancin Amurka da kokarin kawo wa bincike cikas a sakamakon hadarin da ya hada da maaikacin diflomasiyya a ranar lahadi.

Wannan lamari ya kara hadasa zaman tankiyar fannin ayyukan diflomasiyya da Kasar Amurka, lokacin da wani ma’aikacin ofishin jakadancin ta yaki tsayawa umurnin dokokin hanya, wanda hakan yayi dalilin banke wani mutum akan babur kuma ya mutu.

Raja Khalid wanda shine mukaddashin atoni janar ya shaidawa babban kotun dake Islamabad cewa ba za’a tsare ko kuma gurfanad da wannan jami’i ba, sabo da yarjejeniyar kasa-da-kasa na aka sawa hannu a Vienna ta tanadi kariya ta musammam ga maaikatan diflomasiyya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG