Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ce-Ce-Ku Ce Kan Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi a Nijar


A hukumance, Hukumar Zabe ta CENI a Jamhuriyar Nijar ta fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi da na jiha-jiha da kansiloli da aka yi a ranar 13 ga watan Disamba inda alkaluma suka nuna Jam’iyya mai mulki ta PNDS ce ta samu rinjayen kujerun da aka yi takara akansu. 

Ko da yake an riga an fidda sakamakon zaben a baya, amma a ranar Laraba 23 ga watan Disamba ne hukumar ta CENI ta fitar da shi a hukumance.

“Jam’iyya ta farko ita ce PNDS tarayya, wadda ta samu kujeru 1,769.” In ji Malam Aladoua Amada, mataimakin shugaban hukumar CENI.

Dangane da sakamakon zaben jiha-jiha, a nan ma jam’iyya mai mulki ta PNDS ce ke gaba kamar yadda ya yi karin haske. Hakazalika a zabukan kansiloli a cewar hukumar ta CENI, jam’iyya mai mulki ta yi ja-gaba.

Sai dai jam’iyyun adawa na korafin cewa magudi kawai aka tafka wajen samun wadannan nasarori. Bana Ibrahim, jami’i a babbar jam’iyyar adawa ta Moden Lumana ya ce cikin daji aka shiga tun da an san cikin birane ba a iya satar kuri'u, a zaben kananan hukumomi da aka yi.

Sai dai hukumar ta CENI ta ce, ba ta da masaniya dangane da wadannan korafe-korafe.

Fitar da sakamakon zaben da hukumar ta CENI ta yi a hukumance a ranar Talata, na zuwa ne, yayin da ya rage ‘yan kwanaki kadan kafin a fara zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a ranar 27 ga watan Disamba.

A yayin babban zaben jam’iyyar PNDS tarayya ta ce za ta sake yi wa jam’iyyun adawa fintinkau, ikrarin da ‘yan adawa suka ce ba za su bari ba.

Mataki na gaba da za a dauka dangane da sakamaakon zaben na kananan hukumomi a cewar hukumar ta CENI, shi ne za a mika shi ga kotun da ke kula da zaben kananan hukumomi, domin tantance ko an yi zaben bisa ka’ida.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00


XS
SM
MD
LG