Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Bayyana Ra'ayoyi Game Da Kubutar Da Yan Matan Chibok 21


Jami'an gwamnatin Najeriya suna ganawa da 'yan matan Chibok su 21 da aka sako alhamis 13 Oktoba,m 2016 a Abuja
Jami'an gwamnatin Najeriya suna ganawa da 'yan matan Chibok su 21 da aka sako alhamis 13 Oktoba,m 2016 a Abuja

A Nigeria, ana ta ci gaba da murna da kuma bayyana ra’ayoyi game da kubutar 21 daga cikin ‘yanmatan nan na Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace, wadanda suka sami ‘yancin kansu har ma suka sadu da mataimakin shugaban kasar, Yemi Osinbajo jiya a Abuja.

Mataimakin shugaban kasar, wanda yace kubutar yaran abin yabawa ce, ya musanta rahottanin dake cewa “ba ni gishiri, in baka manda” aka yi tsakanin gwamnati da ‘yan Boko Haram, inda aka saki wasu kwamandoji hudu na BH din kafin su kuma su sako ‘yan matan.

Shima ministan watasa labaran Nigeria Lai Mohammed ya dora nasarar samo ‘yanmatan akan abinda ya kira “cijewar da aka yi wajen gudanarda tattaunawa da sulhuntawan da suka haifar da aminci” ne a tsakanin saassan biyu (gwamnati da BH.)

Rahottani sunce kungiyar bada agaji ta Red Cross da gwamnatin kasar Switzerland ne suka jagoranci tattaunawar da ta kai aka sako ‘yanmatan, kuma hukumomin na Nigeria sunce za’a ci gaba da tattaunawar don neman kubutar da sauran ‘yanmatan da suka rage a tsare a hannun ‘yan BH.

Tun a watan Afrilun 2014 ne dai mayakan BH suka yi awon gaba da ‘yanmatan su kusan 300 daga wata makarantar sakandare dake garin na Chibok a jihar Borno. Da yawansu sun samu sun gudu, amma dai har yanzu akwai 219 a tsare.

XS
SM
MD
LG