Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Fafatawa A Libiya


A Libya an cigaba da fafatawa a yau Asabar domin samun damar iko da Ma’adanar Man fetur dake kewayeda Birnin Benghazi

Dakarun Kasa na gabashin Libya wadanda akewa lakabi da LNA a takaice sun hakura da wani babban bangare na gabar ruwa na mahakar man da suka kama a bara a jiya Juma’a.

Janyewar ta biyo bayan wani babban hari da kungiyar da akafi sani da suna Benghazi Defense Bridgades ko kuma BDB a takaice.

Mai Magana da yawun Dakarun Libya na LNA Ahmed AL-Mismari ya fadawa kamfanin dillancin labarai ta Reuters cewa sojojin nasu sun kai dauki a harin da aka kai na gabar teku da Jiragen Sama a Ras Lanuf, da Es Sidra da Ben Jawa da kuma Harawa.

Mismari ya da cewa “Maharan sun kai harin ne a Tankoki na zamani masu dauke da makamai amma har yanzu ana kan fafatawa.”

Yunkurin iko da gabar tekun Mai ta Libya ya kara tayar da yiwuwar mummunan tashin hankali a yankin.

Bayan Sojojin gwamnatin Libya sun kwace gabar a watan Satumbar bara , Aiyukan hakar Mai na Loibya ya kara habaka, wanda hakan ya haifar da matsaloli ga jami’an dake rike da gwamnati a Tripoli wadanda MDD ke goyawa baya.

Gwamnatin da Kasashen duniya ke marawa baya na rike da ikon wani bangare na Tripoli, a yayin da Abokan adawa key akin rike iko da sauran bangarorin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG