Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Muhawara Kan Badakalar Kudaden Yankin Niger Delta


Majalisar dokokin Najeriya
Majalisar dokokin Najeriya

A Najeriya kwararru na ci gaba da tafka muhawara akan badakalar biliyoyin kudi da Majalisar Dokokin kasar ta binciko a hukumar kula da yankin Niger Delta.

A Najeriya ana ci gaba da cece-ku-ce akan batun binciken badakalar biliyoyin Naira da Majalisar Dokoki ta gano a hukumar da ke kula da yankin Niger Delta, abinda ke nuni da cewa dara ce za ta ci gida domin ‘yan jam’iyyar APC ne ke barazanar gurfanar da junansu a gaban kotu.

Batu na baya bayan nan shi ne wanda kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamilla ya bada umurnin shigar da kara akan Ministan Ma'aikatar Niger Delta Godswill Akpabio muddun ya gaza kawo hujja akan ikirarin da yayi cewa ‘yan Majalisa ne suke karbe kwangilolin Hukumar ta NDDC.

To sai dai kwararru a fannin sha'ria da ma wasu 'yan jam’iyyar APC sun bayyana ra'ayinsu akan tanadin da kundin tsarin mulkin kasa ya yi akan irin wannan yanayi da jam’iyyar ta tsinci kanta a ciki, inda kwararre a fannin kundin tsarin mulkin kasa Barista Mainasara Ibrahim Umar ya ce sashi na 36 na kundin tsarin mulki ya ba kowa dama na neman hakkinsa a kotu idan an yi masa ba daidai ba, ko an muzguna masa akan wani abu da ba a tabbatar ba.

Shi ma Barista Nura Danbatta ya kara jadadda cewa majalisa ta na da hurumin neman hakkinta musamman ma wanda ya jibanci bata masu suna, amma tunda Minista Godswill Akpabio ya yi nadama ya ce ba haka ya ke nufi ba, to 'yan majalisa ya kamata su janye maganar su rabu da Akpabio, su fuskanci aikinsu.

Amma daya daga cikin 'yan jam’iyyar kuma shugaban tsare-tsare na gundumar Gwange a Jihar Yobe, Saleh Bakoro Sabon Fegi, ya na ganin shugabannin Majalisar su yi hattara wajan kalubalantar junansu a fili, saboda tamkar suna burma wa cikinsu wuka ne.

Saleh ya ce ya kamata su sulhunta matsalolinsu a cikin gida ba lallai dole sai mutane sun ji abinda ke tsakaninsu ba, duk da haka idan ta tabbata cewa an muzguna wa mutum, to fa ya na iya neman hakkinsa a gaban kuliya.

Ita kuwa Majalisar Dattawa umurni ta ba ma'aikatan hukumar Niger Delta akan su maida wa asusun gwamnati Naira biliyan 1.336 da suka rarraba wa kansu, akan dalilin kalubalantar cutar coronavirus.

Saurari cikakken rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG