Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana cigaba da matsalar karancin man fetur a yammacin Najeriya


Matsalar karancin man fetur a yammacin Najeriya
Matsalar karancin man fetur a yammacin Najeriya

Matsalar karancin man fetur na cigaba a jihohin yammacin Najeriya inda har yanzu ana sayar dashi da tsada

A Ibadan fadar gwamnatin jihar Oyo har yanzu ana fama da karanci man fetur tare da samunshi da tsada.

A wasu gidajen man dake cikin birnin Ibadan suna sayar da man da tsada fiye da farashin da gwamnati ta tsayar na Nera tamanin da biyar kan kowace lita daya. Wadanda suke sayar da man sukan sayar akan Nera dari da goma ko da ashirin ko kuma fiye da haka.

Wadanda suke sayarwa akan farashen gwamnati sai sun tambayi mutum na goro kafin su sayar mashi bayan kashe lokaci a dogon layi..

Alhaji Abdulrahim Abdulrazak shugaban kungiyar masu sayar da man fetur dake zaman kansu ya bayyana dalilin tsadar man. Yace da zara sun sami mai daga dapo na gwamnati zasu sayar akan farashin gwamnati. Wanda suke sayarwa yanzu daga masu zaman kansu suke sayowa.

Masu ababen hawa sun koka da lamarin kana sun roki gwamnati da ta sa baki.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00

XS
SM
MD
LG