Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci gaba Da Zanga Zangar Neman Maduro Ya Sauka a Mulki


Zanga Zanga A Venezuela

Masu adawa da gwamnatin kasar Venezuela sun lashi takobin ci gaba da yin zanga-zanga yau Alhamis don tilastawa shugaba Nicolas Maduro sauka daga kan kujerar mulki.

Dubban ‘yan kasar Venezuela sun dunguma kan manyan titunan Caracas a jiya Laraba, tare da gungun masu goyon bayan Maduro, da kuma masu adawa da shi da manufofinsa na gurguzu.

Jami’an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa a wata unguwa dake yammacin babban birnin kasar. Kuma wani matashi da aka harba a kai a kusa da wurin da aka yi zanga-zangar nuna adawa da gwamnati, ya rasu a lokaci da yake dakin fida.

An dai dora laifin mutuwar matashin akan bangaren masu goyon bayan gwamnati, da kuma kisan wata mata a San Cristobal. Yanzu haka dai ana gudanar da bincike akan kashe-kashen da aka yi.

An sami rahoton kisan wani dogarin wanzar da zaman lafiya a lokacin zanga-zangar a jihar Miranda, kusa da Caracas.

Idan aka hada mace-macen da suka faru jiya Laraba da kuma wadanda suka faru a cikin makonni 3 da aka kwashe ana zanga-zanga adadin mamatan sun kai 8 kenan.

Facebook Forum

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG