Accessibility links

Ana fargaban yiwuwar kashe fursunoni a kasar Gambiya


Wata zanga zangar adawa da muzantawa 'yan jarida a kasar Gambiya
Cibiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta bayyana fargabar cewa watakila aga karin kashe-kashen mutanen da akan yankewa hukuncin kisa a kasar Gambia, bayan mutane tara, fursunonin da aka rataye shekaranjiya Alhamis – wanda kuma shine karo na farko da aka aiwatar da irin wannan hukuncin kisan a cikin fiye da shekaru 25 a wannan ‘yar karamar kasar dake nahiyar Afrika ta Yamma.

Hukumomin Gambia sunki yin wani sharhi game da wannan rahoton da Amnesty ta bada game da wadanan mutanen 9 da aka yanke wa hukuncin kisan, wadanda suka hada maza 8 da mace 1.

A cikin wani jawabin da yawa al’ummar kasar tashi ta tashoshin TV a ran 19 da 20 ga watan nan na Agusta ne, shugaban Gambia Yahya Jammeh yake cewa gwamnatinsa zata aiwatar da hukuncin kisa akan dukkan fursunonin da aka yankewa wannan hukumcini kafin nan da tsakiyar watan Satumba.

Kafin wannan jawabin, ana kiyasin cewa kotunan Gambia sun yanke hukuncin kisa akan jimillar mutane 47, da yawansu mutane ne da aka tuhume su da laifin yiwa kasar zagon kasa.
XS
SM
MD
LG