Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Gudanar Da Zabe A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya


'Yan gudun hijiya a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya

Masu kada kuria sun tafi runfunar zabe a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya bayan shekaru uku ana dage zabe.

Jiya Laraba a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, 'yan kasar suka je rumfunan zabe, domin kada kuri'a a zaben kasar da aka sha jinkirtawa, wanda mutane da dama suke fatar zai kawo karshen tarzomar da ake yi shekaru uku ana fama da ita a kasar.

Anga dogayen layuka a Bangui babban birnin kasar, kodashike akwai rahotanni ba'a bude wasu rumfunan zabe akan lokaci ba, duk da haka babu rahotannin anyi arangama ko magudi ba.

An tsananta matakan tsaro a zaben shugaban kasa da 'yan majalisar, da aka shiry za'a yi tun farko ranar Lahadi, amma aka dage da kwanaki uku saboda matsaloli jigilar kayan aiki da kuma kimtsawa.

XS
SM
MD
LG