Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Harsashen Samun Karanci Abinci


Shanun Huda
Shanun Huda

Kungiyar manoma a Najeriya tayi harashen samun koma baya a fannin noma a wannan shekarar a shiyyar arewa maso gabas

Kungiyar manoma a Najeriya tayi harashen samun koma baya a fannin noma a wannan shekarar a shiyyar arewa maso gabas, sanadiyyar tabarbarewar matsalar tsaro.

Sakataren watsa labarai na kungiyar,Alhaji Muhammad Magaji ne ya shaida hakan a taron maneama labarai a garin Gombe,ciki harda wakilin muryar Amurka,Abdulwahab Muhammad.

Ya bukaci gwamanatin tarayya dana jihohi dasu bulloda wata dabarar da zai toshe gibin daza a samu a kakar noman bana.

Ya kara da cewa “wannan babban matsalace a halin da ake ciki a kasar na ana zaune lafiya ma yaushe manoma suka samu sukayi noma balle ace babu zaman lafiya,kullum yanda ake fadi in babu zaman lafiya babu abunda za’a iya yi ko addini saboda haka wannan ya shafi noma da kiwon kware,an riga an tarwatsa kauyukansu sun waste, ta inna zasu samu suje noma, saboda haka wanna abun da yake faruwa ya kawo wa noma cikas masammam arewa maso gabas ko shakka babu zai shafi kokarin da akeyi na samar da abinci isashe.”

Yana kuma mai jadada cewa a taimakawa manoma da yankinsu suke zaune lafiya domin su kara yawan abunda suke nomawa saboda cike gibin wadanda ke da matsala.
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:17 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG