Zaben Shugaban kasa da na Majalisar Dokokin Tarayyar kasar Kongo, wanda ya fuskanci jinkiri sosai, a karshe dai an fara shi yau dinnan Lahadi, to amma masu lura da al'amura na ganin zaben zai gamu da rudu da kuma tashin hankali a wurare da dama.
Kasar mai arzikin ma'adanai, wadda girmanta ya kai sulusi biyu na fadin yammacin Turai, amma ba ta da wadatattun hanyoyi da sauran madafun rayuwa, ba ta taba samun sabuwar gwamnati cikin lumana ba, tun bayan da ta zama 'yantacciyar kasa shekaru 60 da su ka gabata.
Rahotannin farko na yau Lahadi sun nuna cewa an makara na tsawon sa'o'i da dama kafin aka bude wasu runfunan zaben.
Dadaddiyar mai nazarin al'amuran Kongo, Stephanie Wolters ta Cibiyar Nazarin Al'amuran Tsaro, ta ce ita ba ta ma damu da irin sakamakon da za a samu ba, kamar yadda ta damu da irin hadarin da masu kada kuri'a wajen miliyan 40 za su shiga a yau dinnan Lahadi.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 27, 2023
Burkina Faso Ta Dakatar Da Kafar Yada Labaran Faransa
-
Maris 27, 2023
Mataimakiyar Shugaban Amurka Ta Fara Ziyarar Aiki A Ghana
-
Maris 26, 2023
Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris Ta Isa Ghana