Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kara Daukan Matakan Wanzar Da Zaman Lafiya a Pilato


Chairs are left abandoned after a car plowed through a holiday parade in Waukesha, Wisconsin.

Rundunar tsaro ta musamman a Jahar Pilato tace ta samadda wassu kayayyakin aiki, kwatankwacin wadanda ake amfani dasu a kasashen da suka ci gaba, wajen gano masu aikata laifi a tsakanin al’umma.

Kakakin rundunar tsaro ta STF a jihar Pilato, Manjo Umar Adam wanda ya sanar da haka, yace rundunarsu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.

A yunkurinta na shawo kan matsalar tsaro, hukumar tsaron farin kaya ta kasa, ta horadda jami’anta kan amfani da makami da dabarun gano masu aikata laifi, ganin yadda ayyukan ‘yan’fashi da makami da masu garkuwa da jama’a ke kara yawaita a wassu sassan Najeriya.

A hirarsa da Muryar Amurka yayin wani taron karawa juna sani, kwamandan rundunar a jihar Nasarawa, Mohammed Gidado Fari yace bayan horarwa daban daban da suka yi wa jami’ansu manya da kanana, yana da yakinin cewa, tsaro zai inganta a fadin Najeriya.

Yayin wata ziyarar gani da ido da jajinta da ya kawo jihar Plato bayan kashe kashen da suka wakana a wadansu sassan jihar da suka janyo asarar rayuka da dama, mataimakin jakadan Amurka a Najeriya, David Young yace Amurka tana bada gudunmuwa don tabbatar da tsaro a Najeriya ta hanyar horadda jami’an tsaro, shirya taron sasanta tsakanin jama’a, da kuma bada tallafin kudi ga ‘yan gudun hijira.

Mr Young ya bayyana irin kokarin da kasar ke yi wajen samarda tsaro a Najeriya yace “mun tallafa wa kungiyoyi daban-daban dake aikin inganta tsaro da zaman sasantawa, abinda muka tabbatar yana taimakawa, muna kuma horadda Jami‘an ‘yan’sanda a Abuja dake aiki a fannoni daban-daban.”

David Young ya kara da cewa, “a yanzu haka mun samadda fiye da dala miliyan dari biyu don tallafawa ‘yan gudun hijira kimanin miliyan biyar a Arewa maso gabashin Najeriya.”

Saurari Rahoton wakiliyarmu Zainab Babaji

Ana kara daukar matakan tsaro a jihar Plato-3:44"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG