Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Yunkurin Kawar da Dokar da Ta Hana 'Yan Majlisar Nijar Neman Kwangila


'Yan Majalisar Dokokin Nijar

Kundun tsarin mulkin kasar Nijar ya haramtawa masu rike da manyan mukaman gwamnati tun daga shugaban kasa har zuwa 'yan majalisar dokokin kasar neman kwangila daga gwamnati ko kuma shiga harkokin kasuwanci

Amma yanzu wani dan majalisar dokokin kasar Alhaji Seidu Hamma mai ra'ayin soke dokar da ta haramta masu karbar kwangila daga gwamnati yana cewa tun farko matakin hanasu kasuwanci kumbiya kumbiya ce ta 'yan boko domin tauye hakkin 'yan kasuwar da suka shiga siyasa.

Yace dokar bata kamata ba. Wadanda suka sa ta sun yi ne idanu rufe domin su samu zuwa majalisa da yawa. Ya nemi a canza dokar domin shi dan kasuwa ne kafin ya shiga siyasa kuma har yanzu shi dan kasuwa ne.

Yace a kasashen Burkina Faso da Benin babu irin wannan dokar. Haka ma Ivory Coast ko Togo duk basu da dokar. Yace yanzu dan majalisar Chadi sai ya nemi kwangila a Nijar ya samu amma shi dan kasa bashi da ikon yin hakan.

A shekarar 2010 bayan an hambarar da gwamnatin Tanja Mammadou wasu jami'an fafutika suka kawo dokar haramtawa 'yan majalisa neman kwangilar gwamnati..

Alhaji Nuhu Muhammadou Arzika na kungiyar NPCL yana kan gaban wadanda suka gabatar da shawarar a wancan lokacin. Yace da idan an samu 'yan majalisa da laifi a sha'anin kasuwanci, idan kotu ta bidesu sai su ce suna da rigar kariya kasancewarsu 'yan majalisa.Dalili ke nan da aka kafa dokar.

A bangaren 'yan majalisa dake korafi da dokar akwai alama suna cigaba da yunkurin nasu. Wai duk dan kasuwa dake cikin majalisa zasu hada hannun su ga bayan dokar.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG