Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Kokarin Shan Kan Bazuwar Ebola a Kasar Guinea


Likitoci suna kokarin shan kan bazuwar Ebola.
Likitoci suna kokarin shan kan bazuwar Ebola.

Gwamnatin kasar Guinea na kokawar neman shan kan bazuwar kwayar mummunar cutar Ebola mai kisa, a yayin da makwafciyar ta , kasar Senegal ta rufe kan iyakokin ta na kudanci da suka hada su.

Gwamnatin kasar Guinea na kokawar neman shan kan bazuwar kwayar mummunar cutar Ebola mai kisa, a yayin da makwafciyar ta , kasar Senegal ta rufe kan iyakokin ta na kudanci da suka hada su.

Likitocin kasar Guinea na cikin gagarumin shirin ko ta kwana bayan da aka tabbatar da mutuwar mutane takwas da cutar ta Ebola, har da mutuwa daya da aka samu a babban birnin kasar wato Conakry mai yawan jama'a kimanin miliyan biyu a kalla.

Kafin a tabbatar da cutar a babban birnin kasar, da farko hukumomi cewa suka yi akasarin wadanda suka kamu da kwayar cutar ta Ebola 'yan yankin karkarar kudu maso gabashin kasar ne.

A kokarin neman yin rigakafin kwayar cutar ta hana ta kaiwa ga jama'ar ta, gwamnatin kasar Senegal ta rufe kan iyakokin ta da Guinea, ta bangaren kudancin yankin Kolda da Kedougou.

Hukumar Lafiya ta Duniya , WHO ko OMS, ta ce mutane 70 sun mutu wasu kuma fiye da dari sun kamu da cutar a kasar Guinea tun da aka samu barkewar zazzafar masassarar da ke sa fitar jini daga jikin bil Adama.

Likitoci sun ce a kasashen Laberiya da Saliyo ma ana jin cewa cutar ta Ebola ce ta halaka mutane 11 a 'yan kwanakin nan.

Ministocin harakokin wajen kasashen yammacin Afirka sun fada a wajen wani babban taron da suka yi a makon jiya cewa barkewar cutar Ebola na yin barazana ga tsaron yankin su.

Kwayar cutar Ebola na saurin yaduwa, kuma alamomin ta sun hada da tsananin zazzabi ko masassara, haraswa da gudawa da fitar jini daga idanu da kunnuwa da hanci da kuma baki.

Likitoci na kira ga masu jinyar marasa lafiya da masu wankan gawa da su takaita yin ma'amala ta kai tsaye da wadanda suka nuna yiwuwar kamuwa da cutar ta Ebola.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG