Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kara Fahimta Gameda Cutar Ebola


Dakin gwaje-gwajen cutar Ebola
Dakin gwaje-gwajen cutar Ebola

Kwayar cutar Ebola, wadda ya barke a Afrika tun shekara ta 1976, daya ne daga cikin su mumunar kwayoyin cututuka da aka sani.

Kwayar cutar Ebola, wadda ya barke a Afrika tun shekara ta 1976, daya ne daga cikin su mumunar kwayoyin cututuka da aka sani.

Yana kawo zubar jini da yawa da kuma karayar wani sashi na jiki. Wanan cutar yana kashe mutane kashi 25-90 da ta taras. Har yanzu, babu wani takamaiman magani na wannan cutar ba.

Mutane suna kamuwa da Ebola daga dabbobi, yawanci daga cin naman da ya kamu da cuta ko kuma ya hadu da kashi ko fitsarin Jemage. Cutar yana yaduwa tawurin ruwan dake jikin mutum, ko kuma amfani da allura da aka yi amfani da ita a jikin wanda yake fama da Ebola. Inji Asibitin Mayo, dake Amurka, mutane sukan kamu da cutar kuma ta wurin shirin gawa domin jana’iza.

Alamun cutar sun hada da zazzabi, ciwon kai, kaikayin makogoro, amai da zawo, kuraje, ciwon kirji da tari, raguwar nauyi da zubar jini.

Kebe marasa lafiya itace hanyar kiyaye karin yaduwar cutar tun da yake babu wani magani na cutar Ebola. Mutanen da aka samu da cutar Ebola suna samun taimako da lura da kuma maganin kare rikicewar cutar. Masana suna kusa da yin allurar rigakafi na wannan cutar.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG