Har yanzu ‘yar gudun hijirar Saudi Arabiya Rahaf Mohammed al-Qunun na ci gaba da fuskantar tashin hankali, yayin da ministar harkokin wajen kasar Australia ta fadawa manema labarai yau Alhamis a Bangkok cewa ba a kai ga cimma yarjejeniyar samar mata mafaka ba tukun.
Ofishin kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya ba al-Qunun, wadda ta rufe kanta a wani Otel a tashar jiragen saman Bangkok don hana jami’ai maida ta kasarta, bayan da ta tserewa iyayanta a Kuwait, matsayin ‘yar gudun hijira, kuma tana fatan samun mafaka a Australia.
Matashiyar ‘yar shekaru 18 da haihuwa, ‘yar asalin kasar Saudiyya, ta ce iyayenta za su kasheta idan aka tilasta mata komowa gida kuma ana sa ran ziyarar da ministar harkokin wajen Australia Marise Payne ta kai Thailand ta yiwu a samu nasara wajen nemar mata mafaka.
Facebook Forum