‘Yan Majalisar Dokokin kasashe takwas da Majalisar Dokokin Kungiyar Tarayyar Turai sun kaddamar da wata kafa ta kasa da kasa ta taka birki ma abin da su ka kira, “babban barazana ga ‘yantattar duniya” wato take taken China karkashin jagorancin jam’iyyarta ta kwaminis.
“An kafa wannan kungiya ne saboda ‘yan majalisun da ke wakiltan mutanen kasashensu su iya yin bayani dalla dalla ma gwamnatocinsu cewa akwai bukatar daukar mataki mafi tsauri kan China,” abin da mai magana da yawun Gamayyar Majalisun Dokokin Kasashe Don Tinkarar China, Sam Armstrong, ya gaya ma Muryar Amurka kenan daga birnin London a wata hira da shi.
(Yinkurin China na janyo Afurka)
Kungiyar ta gabatar da kanta ga duniya a ranar Alhamis ta wani bidiyo mai tsawon minti biyu da ke nuna ‘yan majalisa daga kasashen Australia da Canada da Jamus da Japan da Norway da Sweden da Burtaniya da Amurka da kuma Majalisar kungiyar Tarayyar Turai. Cikin sa’o’i kasa da 24 mutane 300,000 su ka karanta kundin bayanin manufar kungiyar da aka buga a yanar gizo, wanda kuma ya janyo tura wata sabuwar tawaga daga Lithuania.
A faifan bidiyon, an ga mambobin kungiyar na tashi daya bayan daya su na karatu da murya mai karfi daga kundin, wanda ke kiran da a dau kwararan matakai kan take taken China a duniya.
Facebook Forum