Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Sukan Shugaban Amurka da Kin Tabo Wasu Manufofin Kasar Lokacin Ziyararsa a Nahiyar Asiya


Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Philipines Rodrigo Duterte wanda yayi kamarin suna wajen kashe dubban mutane da ake zarginsu da safarar miyagun kwayoui ba tare da an yi masu shari'a ba

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama da masu rajin 'yancin 'yan jarida sun zargi Donald Trump da amincewa da gwamnatocin dake take hakkin 'yan Adam da na 'yan jarida a nahiyar Asiya saboda ya ki ya ambato manufar Amurka akan wadannan abubuwa

Masu suka na zargin Shugaban Amurka Donald Trump da kin tabo wasu daga cikin manufofin Amurka irinsu ‘yancin dana dam da ‘yancin jaridanci a ziyarar da ya kai Asiya kwanan nan.

A soke-soken da su ka yi dabam-dabam, kungiyar rajin kare dana dam ta Human Rights Watch da kungiyar ‘yan jarida ta Reporters Without Borders sun zargi Trump da yin na’am da tauye ‘yancin dan adam da yin karan tsaye ga aikin jarida a wasu daga cikin kasashen Asiya da su ka yi kaurin suna wajen mulkin kama karya.

“Kusan dai a yanzu Amurka ta rasa katabus kan batun ‘yancin dana dam,” a cewar Daraktan kungiyar a shiyyar Asiya ga Muryar Amurka.

Daniel Bastar, Shugaban kungiyar ‘yan jaridun ya kara da cewa, “Shugaba Donald Trump na baiwa Shugabannin yankin masu kama karya kwarin gwiwar aika-aikarsu.”

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG