Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tantance Wanda Zai Zama Jakadan Amurka a Sudan ta Kudu


Shugaban Majalisar Dattawan Amurka, Mitch McConnell,
Shugaban Majalisar Dattawan Amurka, Mitch McConnell,

Kwamitin majalisar dattawan Amurka dake kula da harkokin waje ya tantance Thomas Hushek wanda Shugaba Trump ya mika sunansa a matsayin wanda zai nada jakadan Amurka a Sudan ta Kudu

Kwamitin kula da harkokin kasashen waje na majilisar dattijan Amurka yayi zama domin ya tantance wanda shugaba Donald Trump ya mika masa sunan sa a matsayin wanda zai zamo jakadan Amurka a kasar Sudan ta Kudu.

A lokacin zaman tantance shi da akayi na rana guda,Thomas Hushek yace a shirye yake ya dauki nauyin wannan aikin duk ko da yake kasar Sudan ta Kudu kasa ce dake da sarkakiyya a harkokin ta.

Sanata Cory Booker dan jamiyyar Democrat daga jihar New Jersey wanda ya taba kai ziyara a kasar ta Sudan ta Kudu ya shaidawa Hushek cewa ya damu kwarai da irin halin da kasar ta Sudan ta Kudu ke ciki, domin an gaza samun wani ci gaba ta fannin samar da zaman lafiya musammam a wannan gwamnatin ta Shugaba Trump data gaza samar da wata manufa ta sadidan akan rikicin kasar wanda yanzu ya shiga shekaru na biyar.

Haka kuma Booker ya bayyana damuwarsa akan yadda kasashe makwata ke yiwa kokarin Amurka zagon kasa ta hanyar kin taimakawa gwamnatin Kirr.

Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya, MDD ya bayyana cewa kasar Uganda ta taimakawa gwamnatin Kirr da makamai kamar yadda Amurka am ta keyi.

Yace Maaikatar tsaro ta kashe kudi har dala miliyan 130 domin horas da jami’ian a kasar Uganda, kamar yadda bincike na ya tabbatar mani, inji Booker.

“Mun bada manya-manyan makamai ciki ko harda jirage masu saukar ungulu da makamai, amma babban damuwar ita ce, an mayar da kayan nan zuwa kasar Uganda daga kasar Sudan ta Kudu, Inji Booker, yace wannan ba mayar da hannun agogo baya ne na kokarin da muke yi a wannan yankin?

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG