Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Taron Neman Hadin Kan Masu Ruwa da Tsaki Kan Yaki da Matsalar Tsaro a Niger


Kalla Mukhtar, ministan tsaron jamhuriyar Niger
Kalla Mukhtar, ministan tsaron jamhuriyar Niger

Wata cibiya dake nazari kan tsaro da binciken dabarun tsaro dake ofishin shugaban kasar Niger ce ta shirya taron na kwana uku game da yadda za'a kirkiro sabbin dabarun yaki da matsalar tsaro a kasar

Taron nazari da binciken dabarun tsaro na kwana uku zai fara ne da soma duba nasarori da irin wahalhalun da aka fuskanta a fannin tsaro daga lokacin da aka kafata ta yadda za'a gyara tafiya a yakin da kasar Niger ta kaddamar da yaki akan ta'addanci.

Mataimakin daraktan cibiyar Abdulaziz Garba ya ce sun gane tsaro ba na hukumar soji ba ne kadai, har da ma al'umma domin daga kansu ya kamata ya fara. Injishi, dalili ke nan da suka tara masu ruwa da tsaki akan harkokin tsaro tare da jama'a daga kowane bangaren kasar su taru su yi nazari na kwana uku. Bayan taron sai su tantance abubuwan da aka fada kana su mikawa gwamnati shawarwarinsu.

Shugaban majalisar karkarar Tawa Adamu Illo dake halartar taron na da kwarin gwuiwar tasirin shawarwarin da za'a fito dasu a karshen taron amma ya gargadi kasashe renon Faransa da su sake salon gudanar da tsaro.

Hukuma ko ta sojoji ko ta 'yan sanda basu isa ba tabbatar da tsaro ba, a cewarsa. Hadin kan jama'a na da mahimmanci wajen cimma nasara a yaki da ta'addanci. Adamu Illo ya yi misali da Najeriya inda ya ce akwai tsaro amma ba'a musgunawa jama'a. Idan wani ya shiga matsala da jami'an tsaro shi ya jawo ma kansa. Kamata ya yi a matsayinsu na kasashe masu 'yancin kai su san yadda zasu gudanar da harkokin tsaronsu ta damawa da jama'a.

Ga rahoton Souley Mummuni Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG